Letexier ne zai yi raflin wasan Real da Chelsea a Champions



Francois Letexier

Asalin hoton, Real Madrid FC

An bayyana Francois Letexier a matakin wadda zai busa wasan Real Madrid da Chelsea ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Real za ta fafata da Chelsea a wasan farko a zagayen quarter finals a gasar zakarun Turai ta Champions League.

Wannan shine karon farko da raflin dan kasar Faransa zai yi alkalancin fafatawar Real Madrid.

Wasa na biyu da zai busa wa Chelsea, bayan wanda kungiyar Stamford Bridge ta ci Dinamo Zagreb 2-1 ranar 2 ga watan Nuwambar 2022.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like