Kasashen na Turai dai ciki kuwa har da Ostiriya da Hangari na cikin kasashe da ke neman Kungiyar EU ta hada kai da kasashen Arewacin Afirka dan mayar da masu neman mafakar siyasa a Turai inda suka fito.

Kasar Libiya da ke zama matattara da ‘yan gudun hijira ke amfani da gabar tekunta dan zuwa Turai ta yi fatali da kiran kasashen na Turai na ta samar da sansanoni na ‘yan gudun hijira a yankunan da ke gabar tekunta, inda kasar ta ce kungiyar ta EU na kokari na kin daukar nauyin da ya rataya a wuyanta ta na neman ta makala wa kasar ta Libiya.
Mohamad Taher Siala ministan harkokin wajen kasar ta Libiya ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a gaban taron Kungiyar hadin kai da tsaro ta Tarayyar Turai a birnin Vienna.
Ya ce wannan kira abu ne da ba zai yiwu ba duba da halin da ake ciki a Libiya da yaki ya daidaita ta da ke kuma neman yadda za ta kawo karshen aiyukan masu ta’addanci da sunan addinin Islama.