Kanar Ahmad Mesmari, mai Magana da yawun kamfanin ya sanar da cewar daga jiya laraba sun mika tashohin na Zuwaytina da Brega da Ras Lanuf da kuma Al Sidra ga kamfanin man kasar dan ci gaba da tafiyar da su.
Firaministan riko Fayez al-Sarraj ya tattauna da shugaban ‘yan tawayen Fil Mashal Khalifa Haftar dan samun wanann nasara.
Rikicin kasar Libya dai ya durkusar da duk wata hanyar samun Kudin shiga a kasar inda ake gani soma fitar da Man a yanzu zai cike wani gibin tattalin arzikin kasar.