Cutar zazzaɓin Lassa ya sake bulla a jihar Kogi bayan da wani likita dake aiki da Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Lokoja aka tabbatar ya kamu da cutar.
Dakta Olatunde Alabi shugaban cibiyar wanda ya yi wa manema labarai jawabi ranar Asabar a Lokoja yace likitan mai shekaru 30 an masa gwajin kwayar cutar ranar 19 ga watan Janairu.
Ya ce samfurin jinin likitan an tura shi dakin gwaje-gwajen kimiyya na Cibiyar Kula Da Lafiya ta Tarayya dake Irua, jihar Edo domin gwaji kuma aka tabbatar yana ɗauke da ƙwayar cutar.
Alabi ya ce likitan mai shekaru 30 da safiyar ranar Asabar an ɗauke shi zuwa Irua domin a cigaba da yi masa magani.
A cewar shugabana asibitin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Ma’aikatar Lafiya ta Jihar da kuma sauran masu ruwa da tsaki an sanar da su halin da ake ciki kuma tuni suka fara tallafawa cibiyar ta hanyoyi iri-iri.
Ya ce dukkanin mutanen da suka haɗu da likitan a gida ko a asibitin suna nan ana sa musu ido.