Likitoci a jihar Kogi sun dakatar da yajin aikin da suka yi na kwanaki 72


Kungiyar Likitoci Ta Najeriya NMA, reshen jihar Kogi ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 72 tana yi domin ba da damar cigaba da tattaunawa da gwamnatin jihar.

Shugaban kungiyar reshen jihar, Dakta Godwin Tijani shine ya fadi haka ranar Talata bayan wani taron gaggawa da kungiyar ta yi a A Lokaja.

Ya ce an dakatar da yajin aikin ne domin girmama shugaban kungiyar NMA na kasa, Farfesa Mike  Ogirima, wanda ya roki kungiyar da ta dakatar da yajin aikin ta kuma cigaba da tattaunawa da gwamnati.

Tijani ya ce majalisar gudanarwar kungiyar ta kuma yi duba ga rokon da jama’a suke yi da kuma soyayyar da likitoci suke da ita ga marasa lafiya kafin su yanke shawarar  dakatar da yajin aikin.

“Dukkanin likitoci da suke aiki da gwamnatin jihar Kogi ana umartarsu da su dawo bakin aiki daga ranar Alhamis 22 ga watan Maris.

” Kungiyar na sa ran gwamnati za ta biya bashin kudin albashi da likitocin su ke bi cikin wata guda mai zuwa  ta kuma yi maganin sauran batutuwa da suka haddasa tafiya yajin aikin domin kaucewa sake tafiya wani sabo.”

You may also like