Likitoci A Jihar Zamfara Sun Sha Alwashin Bazasu Qara Duba ‘Yan Sanda Da Iyalansu Ba



Kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar Zamfara, NMA ta dau alwashin ba za ta sake duba lafiyar jami’an ‘yan sanda da Iyalansuba a dukkanin asbitoci dake fadin jihar Zamfara. 
Kungiyar ta bayyana daukan wannan mataki ne akan cin zarafin ma’aikatanta da take zargin wasu ‘yan sanda sun yi alhali yana kan aiki.
Kungiyar liktocin ta dade tana takun saka da ‘yan sanda a jihar, tun bayan zargin lakadawa ma’aikatanta kashi da ake zargin ‘yan sandan da yi akan cewa ya hau babur da dare duk da dokar da aka kakaba na hana zirga-zirgar babura a jihar Zamfara daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe sama da shekara biyu. 
Kamar dai yadda shugabannin Kungiyar Tijjani Abubakar, Shugaba da sekatarensa Mannir Bature suka bayyana, Kungiyar ta bayyana ta dau matakai na shari’a kafin daukan wannan mataki amma abubuwa sun ci tura, suna baukatar sai an baiwa ma’aikatanta da aka ciwa mutunci hakkinsu. 
Tuni dai Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Zamfara Mista Shaba Alkali ya roki likitocin da su janye wannan mataki nasu a cigaba da zaman sulhu, kasancewarsa shi sabon zuwane a jihar kuma bai jima da kama aikiba. 
Tuni dai al’ummar jihar Zamfara suka fara kiraye kiraye ga gwamnatin jihar Zamfara akan ta jaye dokar takaita zirga-zirgar babura dake cigaba da gudana a jihar kasancewar yanzu an samu saukin matsalar tsaro a jihar.

You may also like