Likitoci Sun Koka Kan Yadda Yan Bindiga ke Yawan Garkuwa Da Abokan Aikinsu A Jihar Rivers Likitoci karkashin kumgiyar likitoci ta (AGPMPN) sun nuna damuwarsu kan yadda ake yawan garkuwa da abokan aikinsu musamman ma a jihar Rivers.

Kungiyar tayi wannan koken ne a taron shugabannin kungiyar na kasa da aka gudanar a karshen mako,shugaban kungiyar na kasa Dr. Omo-Ehijele Frank Odafen,yayi Allawadai kan yadda ake yawan yin garkuwa da likitocin,inda yace da yawa daga cikin abokan aikinsu sun rasa rayukansu a hannun masu garkuwa da mutane.

Dakta odafen wanda yayi magana da yan Jaridu yace lokaci yayi da gwamnati da kuma hukumomin tsaro za su fara hada likitoci da jami’an tsaro dauke da makamai domin gudanar da aikinsu ba tare da fargabar sace su ba ko kuma su rasa ransu. 

Yace “Likitoci mutane ne da suka bada himma wajen samar da aiyukan jinkai ga jama’ar  kasa. Muna rokon al’umma da kuma masu garkuwa da mutane da su kyale likitoci,  bamu da kudi muma mutane da muke fafutukar samun na cin abinci, muna kira ga gwamnati musamman ma ta jihar Rivers, da tabbatar da cewa an kare likitoci.” 

You may also like