Likitoci sun raba jarirai dake makale da juna a Yola


Wata tawagar kwararrun likitocin dake Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Yola, sun samu nasarar raba wasu jarirai yan biyu dake manne da juna.

Auwal Abubakar shugaban cibiyar ya ce an samu nasarar yin aikin tiyatar a ranar 14 ga watan Mayu.

Da yake magana da manema labarai a birnin Yola, Auwal ya ce kwararrun likitocin sun shafe sa’o’i hudu suna aikin tiyatar.

Abubakar ya kara da cewa akwai cikakken kwarin gwiwa cewa yan biyu za su cigaba da rayuwa.

Ya kuma yi kira da hada hannu wajen rage yawan zuwa neman lafiya kasashen waje.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like