Hadin Kan Musulmi Wajibi Ne Domin Fuskantar Makiya
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran ya ce: Wajibi ne ga musulmi da su hada kawukansu domin tsayin daka wajen fuskantar makiyan addininsu.
Ayatullah Muhammad Imami Kashani, ya bayyana cewa; Wajibi ne ga musulmi su zama cikin fadaka su kuma hada kai domin kalubalantar wadanda su ke son rusasu.
Ayatullah Muhammad Imami Kashani ya ci gaba da cewa; Daya daga cikin manufofin makiya shi ne raba musulmi da koyarwar addininsu, sanann ya kara da cewa: Domin cimma wannan manufar ta makiya suna kokarin fassara musulunci ta hanyoyi daban-daban.