Lionel Messi ya ce zai yi ban kwana da gasar cin kofin duniya



Messi

Asalin hoton, Getty Images

Kyaftin din kwallon Argentina, Lionel Messi ya ce daga wasan karshe na gasar cin kofin duniya a ranar Lahadi ba zai kara buga gasar cin kofin duniya ba.

Kawo yanzu, dan kwallon mai shekaru talatin da biyar ya ci kwallo biyar a gasar da ake buga wa a Qatar.

Duk da cewa sau biyar yana halartar gasar cin kofin duniya, amma har yanzu bai taba lashe gasar gasar.

“Ina murna zan kammala wannan gasar a matakin wasan karshe. Abun jindadi ne”, in ji Messi.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like