
Asalin hoton, Getty Images
Jarrad Branthwaite
Liverpool na cikin ƙungiyoyin da suka nuna sha’awarsu kan ɗan wasan Everton Jarrad Branthwaite, 20, wanda yake a matsayin aro a PSV Eindhoven. Manchester United da Roma ma na kwaɗayin sayen ɗan wasan na Ingila da ke taka leda a ƙungiyar ƴan ƙasa da shekara 20. (Mail)
Ɗan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, 33, na dab da barin Chelsea zuwa Los Angeles FC. (Le10 Sport, via Metro)
Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Chelsea da Thiago Silva kan tsawaita kwantiraginsa har bayan ranar da yake cika shekara 39 da haihuwa cikin watan Satumba. (London Evening Standard)
Arsenal da Liverpool da Newcastle sun nuna sha’awarsu ta son sayen ɗan wasan tsakiya na Mexico da ke buga wa Ajax, Edson Alvarez, 25. (Caught Offside)
Arsenal na iya bazama domin zawarcin mai buga wa Real Sociedad kuma ɗan wasan tsakiya na Spaniya, Martin Zubimendi, 24, a bazara ganin cewa hankalin Barcelona ya karkata wani wajen. (Mirror)
Rahotanni na cewa Ɗan wasan Borussia Dortmund mai buga wa Ingila tsakiya Jude Bellingham, 19, ya soke yiwuwar komawa Chelsea da Paris St-Germain bazara. Liverpool da Barcelona da Real Madrid da Manchester City da Manchester United na rige-rige a kan ɗan wasan. (Express)
Everton za ta sake yunƙurin sayen ɗan wasan gaba na Portugal Beto, 25, daga Udinese a bazara bayan da aka gaza ƙulla kwantiragi a Janairu. (Mondo Udinese – in Italian)
Kocin Spaniya Andoni Iraola, 40, ya yi fatali da buƙatar Leeds United don ya maye gurbin Jesse Marsch da aka kora yayin da kulob ɗin ke ci gaba da fuskantar ƙalubale a ƙoƙarinsu na naɗa sabon koci. (Onda Cero, via Express)
Tottenham na iya zawarcin tsohon golan Manchester United da Ingila, Ben Foster domin cike gurbin Hugo Lloris wanda ba zai buga wasa ba tsawon mako shida saboda raunin da ya ji. Foster ya sanar da rataye takalminsa a Satumban bara amma yana iya zuwa ƙungiyar a matsayin aro na gajeren lokaci. (Mirror)
Chelsea ta yanke shawarar ɗaukan Andrey Santos, 18, a matsayin aro zuwa wani kulob ɗin Brazil ko da ya gaza samun takardar izinin aiki. Ɗan wasan Brazil na ƴan ƙasa da shekara 20 ɗaya ne daga cikin ƴan wasa takwas da aka saya a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa a Janairu mai cike da tarihi inda ya koma kulob ɗin kan £16m daga Vasco da Gama. (London Evening Standard)
An ƙarfafa wa Man United gwiwa a zawarcin da take kan ɗan wasan Barcelona Frenkie de Jong, 25, da ɗan wasan gaba na Spaniya Ansu Fati, 20, inda La Liga ta buƙaci ƙungiyar ta rage musu albashi. (Mundo Deportivo, via Mail)
Tsohon ɗan wasan Arsenal Olivier Giroud zai tattauna batun sabon kwantoiragi da AC Milan. Ɗan wasan Faransar mai shekara 36 ya kasance wanda idon Everton ke kansa a Janairu. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasa Joao Mendes, ɗa ga fitaccen ɗan wasan Brazil Ronaldinho, na shirin komawa Barcelona bayan da ya yi nasarar tsallake gwaji a Nou Camp. (Star)
Ɗan wasan Morocco da ya haska a gasar kofin duniya Sofyan Amrabat, 26, ya yi tayin ya buga wasa kyauta domin ya samu damar komawa Barcelona daga Fiorentina. (Mundo Deportivo, via Sun)