
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta fara shirin sake gina kan ta a kakar wasan lokacin bazara, sun fara zura ido kan dan wasan Real Madrid kuma na tsakiyar Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 23. (El Nacional – in Catalan)
Newcastle da West Ham na sahun gaba a son dauko dan wasan Ivory Coast winger Wilfried Zaha, mai shekara 30, a kyauta, idan kwantiraginsa da kungiyar Crystal Palace ya zo karshe a lokacin bazara. (Star)
Newcastle ta dade ta na sanya ido kan dan wasan Manchester United Scott McTominay sai dai Man United ta sanya burin fam miliyan 50 akan dan wasan tsakiyar na Scotland mai shekara 26. (Star)
Ta tabbata Manchester United da Chelsea na zawarcin dan wasa Victor Osimhen, sai dai dan wasan mai kai hari na Najeriya, mai shekara 26 ya ce ya na jin dadin zama Napoli. (France Football, via L’Equipe)
Manchester United na fatan dauko Harry Kane a kakar wasan nan, tun bayan janyewar Bayern Munich daga kokawar daukar dan wasan, sai dai Tottenham na bukatar fam miliyan 100 kan mai kai harin na Ingila dan shekara 29. (Mirror)
Arsenal na son dan wasan baya na Jamus Ridle Baku, mai shekara 25, sai dai za su fafata da kungiyoyin Chelsea da Villarreal a zawarcin dan wasan. (Caught Offside)
Tsohon shugaban kungiyar Leeds Jesse Marsch ya amince da kwantiragin aiki Leicester City kan matakin dogon zango, bayan kin amincewa da tayin Southampton a watan Fabrairu kan tayin aiki da shi zuwa karshen kakar wasa. (Mirror)
Barcelona ta dakatar da tattaunawa kan sabon kwantiragin daukar Ousmane Dembele saboda sun gagara kara farashi kan dan wasan na Faransa mai shekara 25. (Sport – in Spanish)
Barca ana sanya ido domin ganin kara bunkasar dan wasan tsakiya na Turkiyya Arda Guler, mai shekara 18.. (Relevo – in Spanish)
Kungiyar kwallon kafar Al Hilal ta kasar Saudiyya, na aiki tkuru domin dauko mai tsaron gida na Sifaniya Sergio Ramos mai shekara 37, wanda kwantiraginsa da Paris St-Germain zai kare a karshen kakar wasa. (Nicolo Schira)
Dan wasan baya na Watford, Harry Amass ya shirya tsaf domin komawa kungiyar Manchester United duk da tayin da Chelsea da Manchester City suka yi na daukar dan wasan. (Football Transfers)
West Ham na son daukar Rafael Benitez a matsayin sabon manajan kungiyar, amma hakan za ta faru idan suka kori David Moyes kafin karshen kakar wasa. (Football Insider)