
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron raga, kyaftin din Tottenham, Hugo Lloris zai yi jinyar mako shida zuwa takwas.
Tsohon kyaftin din tawagar Faransa, mai shekara 36 ya buga wasan da Tottenham ta ci Manchester City 1-0 a gasar Premier ranar Lahadi.
Tottenham tana da tsohon golan Southampton mai tsare ragar tawagar Ingila, Fraser Forster wanda zai maye gurbinsa.
Haka kuma tana da masu tsaron raga matasa daga karamar kungiyar da ya hada da Brandon Austin da Alfie Whiteman, sai dai ba su da kwarewa a manyan wasanni.
Tottenham wadda take ta biyar a teburin Premier League a kakar nan, na kokarin neman gurbin shiga Champions League na badi.
Ranar Asabar Tottenham za ta kara da Leicester City a Premier League daga nan ta ziyarci AC Milan
Ranar Talata Milan za ta karbi bakuncin kungiyar Ingila, domin buga wasan farko na kungiyoyi 16 a Champions League na bana.