
Asalin hoton, Getty Images
Yara da dama sukan nuna sha’awarsu ga yin azumi domin suna jin cewa sun fara girma
Azumi wata ibada ce da take zama wajibi a kan dukkan musulmi mace da namiji da ya kai munzalin yin ta.
Ya kan zama wajibi ga lafiyayyen Musulmi mai cikakken hankali da ya kai shekarun balaga.
Wannan ya sa iyaye da dama suke fara ko yawa ‘ya’yansu yin azumu tun suna da ƙananan shekaru, lokacin da za su kai shekarun da ya wajaba a kansu ba za su sha wuya ba.
BBC ta tattauna da Malam Ibrahim Suraj Adhama na’ibin masallacin juma’a na unguwar Gama da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano, domin jin halaccin hakan a mahangar addinin musulunci.
Shi azumi mi ba kamar sallah ba ne da Annabi Muhammad ya ce a fara koyawa yara a wasu tsayayyun shekaru ba.
A sallah Annabi ya ce “ku umarci ‘ya’yanku da su fara sallah idan sun kai shekara bakwai, ku dake su idan suka ƙi yi idan sun kai shekara 10,” in ji Malam.
Shi azumin a iya sanina, ba shi da wannan iyakancewar umarnin yara su fara azumi a shekaru kaza, wataƙila hakan ba ya rasa nasaba da cewa shi abu ne mai wuya sama da sallah.
“Ko manya sun san azumi abu ne mai whala, shi yasa Ubangiji ya ce shi ke biyan ladan azumi da kansa.
“A fahimta ta, bai wa yaro ƙarami damar gwada azumi ta danganta ne da yadda yaron ya fara nuna sha’awarsa kan azumin,” in ji Malam Adhama.
Amma idan ya ce yana son yi sai a ba shi dama a riƙa ɗan sa masa idanu, amma da ya ji ya gaji ba zai iya kaiwa ba sai a bashi damar ajiyewa ganin cewa bai wajaba a kansa ba.
Akan ba shi dama ya yi na rabin rana kamar ace masa ƙarfe biyu zai sha ruwa, idan biyu ta yi sai a ba shi abinci ya ci gudun kada ya galabaita.
Gobe ma idan ya ƙara ɗauka ya kai ƙarfe biyun sai a haɗa da na jiya ya yi ɗaya kenan, Malam ya faɗa cikin murmushi.
“Abu na gaba da zai iya taimakawa shi ne, yanayin girman jikin yaron da kuma yanayin gari da ake azumi a ciki.
“Idan ana sanyi yaron zai fi jin daɗin azumin, idan kuma irin yanayin da ake ciki a garuruwa irinsu Kano da Yobe da Adama da Borno ne to gaskiya ba za mu bayar da shawarar a riƙa barinsu suna azumin ba ko da na rabin rana.
“Dattijai ma da mutane masu rauni cewa ake su ajiye azumi ina kuma ga ƙaramin yaro, sai ya zama cutarwa a gare shi. Maimakon ya riƙa sha’awar ƙara yi sai ya ji ya ma tsani azumin baki ɗaya.
“Ka ga ba a cimma manufar ba shi damar ba kenan,” in ji Malam Ibrahim Suraj.
Ya ce azumi lokacin sanyi ko damuna shi ne daidai da bai wa yaran dama su gwada karfinsu da jarumtarsu kan azumin.
A baya ana bai wa yara damar fara azumi tun suna ‘yan shekara 10, sai kaga yaro ya yi azumi goma sha, gabanin ya balaga.
Lokacin da zai balaga dama ya saba da azumin kawai ci gaba zai yi da yin abinsa.