Obasanjon ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis din da ta gabata a jihar Legas, wajen kaddamar da wani littafi da lakcara mace ta farko a Nijeriya Farfesa Bolanle Awe ta rubuta mai taken “Nigerian Women Pioneers and Icons” ma’ana “Matan Nijeriya: Magabata da Jagorori”
Ya ci gaba da cewa “Duniya a halin yanzu na fuskantar wani canji inda mata ke jagorantar al’ummarsu, a saboda haka bai kamata a bar Nijeriya a baya ba”.
Tsohon shugaban na Nijeriya ya bada misali da kasar Birtaniya inda mace ta dare karagar mulkin kasar da kuma yadda alamu ke gwada cewa Amurka ma mace ce za ta mulki kasar a zabukan da za a yi a watan Nuwamban bana wanda zai tabbatar da Hillary Clinton mace ta farko ta zama shugabar kasar Amurka
“Yanzu ne lokacin da ya dace mata su amfana da irin gudunmawar da mata magabata kuma jagorori suka bayar wajen gina kasar Nijeriya”, Obasanjon ya ce. “Mata a Nijeriya suna matukar bada gudunmawa wajen ciyar da kasar nan gaba a saboda haka ya dace a karo na farko ‘yan Nijeriya su zabi mace don zama gwamnar wata jihar”.
“Mata na da hakuri da juriya bugu da kari kuma sun bazu a dukkanin harkokin ci gaban kasa. Nan gaba kadan za mu fara samun mata a matsayin zababbun gwamnoni a Nijeriya”. A cewar Obasanjo ta bakin Dakta Femi Majekodunmi wacce ta wakilce shi a taron