Luis Enrique ya yi takaicin rashin jagorantar Chelsea, Arsenal na zawarcin Vlahovic



Luis Enrique

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta gana da tsohon manajan Bayern Munich Julian Nagelsmann, a kokarin da suke ni na neman gwarzon shugaba, bayan korar Graham Potter. (Times – subscription required)

Tsohon manajan Sifaniya Luis Enrique, bai ji dadi ba kan rashin nasarar jagorantar Chelsea gabannin kungiyar ta kai bantenta a wasan gab da na karshe na gasar Champions League bayan lallasa Real Madrid, Sai dai ana samun rahotannin zai iya taimakawa wajen dauko dan wasan Barcelona kuma na tsakiyar Sifaniya mai shekara 18 wato Gavi. (AS – in Spanish)

Real Madrid na son amfani da dama wajen dauko dan wasan tsakiya na Manchester City Erling Haaland, domin dauko mai kai harin na Norway a shekarar 2024.(Fichajes – in Spanish)

Arsenal na yunkurin dauko dan wasan Juventus, Dusan Vlahovic mai shekara 23, da kuma dan wasan Everton na tsakiyar Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 26,a matsayin kar ta kwana idan ba su samu damar daukar dan wasan Sabiyan. (Football Insider)



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like