
Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran dan kwallon Liverpool, Luiz Diaz zai yi jinyar wata uku, bayan da likitoci suka yi masa aiki.
Diaz, mai shekara 25 ya koma atisaye, bayan jinyar rauni da ya ji a gwiwar kafa a karawar da Arsenal ta ci Liverpool 3-2 a cikin watan Oktoba.
Dan wasan tawagar Colombia ya fama raunin ne a wasan atisayen Liverpool a Dubai.
Tun farko kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce raunin koma baya ne ga kungiyar Anfield.
”Raunin abin takaici ne ga kungiyar da shi kansa dan kwallon.”
Liverpool tana ta shida a Premier League, bayan wasa 14 daga nan aka yi hutun zuwa buga Gasar Kofin Duniya a Qatar da aka fara 20 ga watan Nuwamba.
Za kuma ta kara da Manchester City a zagaye na hudu a Carabao Cup ranar 22 ga watan Disamba.
Liverpool za ta buga wasan Premier League da Aston Villa ranar 26 ga watan Disamba, bayan hutun kammala Gasar Kofin Duniya.
Za a buga wasan karshe a babbar Gasar tamaula ta Duniya ranar Lahadi tsakanin Argentin da duk wadda ta yi nasara tsakanin Faransa da Morocco ranar Laraba.