
Asalin hoton, EPA
Romelu Lukaku ya zira ƙwallaye huɗu a rabin lokaci na farko yayin da Belgium ta lallasa Azerbaijan da ci 5-0 a wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2024.
Ɗan wasan mai shekara 30 yana da ƙwallaye 83 a wasanni 113 da ya buga wa Belgium, wanda hakan ya sa ya zama na bakwai mafi yawan zira ƙwallo a raga a tawagar ƙwallon kafar ƙasa a duniya.
Cristiano Ronaldo (128 a Portugal) da Ali Daei (109 a Iran) da Lionel Messi (106 a Argentina) da Sunil Chhetri (93 a Indiya) da Mokhtar Dahari (89 a Malaysia) da kuma Ferenc Puskas (84 da Hungary) ne waɗanda suka fi Lukaku zira wa ƙsarasu ƙwallaye a wasan ƙwallon ƙafa na duniya.
Tuni Belgium ta tabbatar da gurbinta a gasar Euro 2024 sannan ta ƙetara Austria, inda ta zama ta ɗaya a rukunin F da wannan nasara.
Ba a doke ta ba tun lokacin da koci Domenico Tedesco ya fara jan ragamar tawagar a watan Fabrairu.