
Asalin hoton, Getty Images
Benfica ta yi rashin nasara a hannun Inter Milan da ci 2-0 a wasan farko zagayen quarter finals a Champions League ranar Talata.
Milan ta ci kwallo farko ta hannun Nicolo Barella, bayan da suka koma karawar zagaye na biyu.
Romelu Lukaku, wanda ke wasannin aro daga Chelsea shine ya zura na biyu a raga a bugun fenariti, saura minti takwas a tashi wasa.
Karo na hudu da suka kece raini a tsakaninsu, inda Inter ta ci uku da canjaras daya.
Wasa tsakanin Benfica da Inter Milan:
Champions League 11 ga watan Afirilu 2023
- Benfica 0 – 2 Inter Milan
UEFA Cup Alhamis 26 ga watan Maris 2004
UEFA Cup Alhamis 11 ga watan Maris 2004
European Cup Alhamis 27 ga watan Mayu 1965
Tun bayan da Benfica ta kai wasan karshe a European Cup a 1990, an fitar da kungiyar Portugal a quarter finals karo biyar a Champions League.
Wannan shine wasan farko da Inter ta kai quarter finals tun bayan shekara 12, tun daga nan ba ta kara abin kirki ba, bayan lashe kofin a 2010.
Kungiyar da Simone Inzaghi ke jan ragama za ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar Laraba 19 ga watan Afirilu a Italiya.