Ma’aikacin Gidan Marigayi Shugaba ‘Yar Adua Ya Zambaci Iyalin Shugaban Har Na Naira Miliyan 91


turai

 

Daya daga cikin ma’aikatan gidan tsohon shugaban Nijeriya mai rasuwa Umar Musa ‘Yar Adua ya tafkawa iyalin marigayin sata na zunzurutun kudi wuri na guga wuri har Naira miliyan 91.

Wannan mutum da ake kira da Yusuf Sarkin Gida wanda ya kasance daya daga cikin amintattun ma’aikatan gidan marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua, ya samu kimanin shekaru 40 yana aiki da gidan na ‘Yar Adua a matsayin Sarkin Gida.

Kwamishin ‘yan sandan jihar Katsina, Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar al’amarin ,inda ya bayyana cewa iyalin ‘Yar Adua sun shigar da kara kafin daga bisani kuma jam’an ‘yan sanda su kama Yusuf Sarkin Gida

A cewar kwamishan ‘yan sanda: “Jami’an ‘yan sanda sun cafke Alhaji Yusuf Sarkin Gida bayan takardar korafi da uwargidan marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar Adua, Hajiya Turai ‘Yar Adua ta shigar makonni biyu da suka gabata.”

Wanda ake zargi dai zuwa yanzu yana hannun ‘yan sanda yana amsa tuhumar da ake masa.

Kwamishinan ‘yan sanda ya ci gaba da cewa: “Shi wanda ake zargi ya kasance shi ke kula da mukullan dakin ajiyar Hajiya Turai tun tsawon shekaru 40 da suka wuce, kuma dakin ajiyar na dauke da akwatuna 37 ne, inda zuwa yanzu 10 daga ciki suka yi batar dabo saura 27 kadai suka rage a dakin.”

“Har ila yau dai, ko akwatuna 27 da suka rage sai da aka bude su aka kwashe wasu daga cikin abubuwan da ke cikinsu”, a cewar kwamishinan ‘yan sandan na Katsina.

You may also like