A wata hira da ya yi da manema labarai da yammacin Jumma’a a Yola shugaban Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa reshen jihar Adamawa (NULGE) Comrade Hamman Jumba Gatugel ya ce, ma’aikatansu ba za su gurfana a gaban kwamitin tantance ma’aikata da majalisar dokokin jihar ta Adamawa ta nada domin tantance ma’aikata ba.
Gatugel ya ce, sun dauki wannan matakin ne sakamakon watsi da su a matsayin ma’aikata da gwamnatin jihar ta Adamawa ta yi, inda ya ce yau watanni biyar kenan rabonsu da albashi, don haka ma’aikatan su dake nesa ba su da kudin mota da za su iya zuwa inda za a yi tantancewar.
Shi ma dai da yake amsa tambaya kan dalilin tantatance ma’aikatan Honarabul Hassan Mamman Barguma shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar ta Adamawa ya ce, sun dauki matakin tantance ma’aikatan ne saboda akwai wadanda suka mutu, ko suka yi ritaya, ko kuma suka canza ma’aikata amma har yanzu albashinsu yana tafiya, kuma bayan sun kammala ne za su tilastawa gwamnati lamba da ta biya ma’aikatan duk wani hakkin da suke bi.
Arewa24news ta yi kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar Adamawa don jin dalilin da ya sa tun shekarar da ta gabata rabonsu da biyan ma’aikatan kananan hukumomi albashinsu, amma hakan ya ci tura, sai dai a wata hira da manema labarai a kwanakin baya kwamishinan yada labarai Ahmad Sajoh ya ce, gwamnatin jihar ba ta manta da ko wani ma’aikaci ba, kuma ba da dadewa ba za ta biya duk wasu ma’aikata da suke bin gwamnati bashi.