Ma’aikatan Jihar Jigawa Sun Fara Karbar Kudin Hutunsu


A Daidai Lokacin Da Ma’aikata Da Dama A Sauran Jihohin Nijeriya Suke Cikin Matsalar Rashin Samun Albashinsu, Lamarin Ya sha Bamban A Jihar Jigawa, Domin Mu A Jihar Jigawa Bayan Biyan Ma’aikata Albashi Akan Kari Duk Wata Har da Karin Biyan Kudun Hutu Duk Shekara.

Tuni Gwamnatin Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Gwamna Alh Muhammad Badaru Abubakar, Ta Fara Biyan Dukkanin Ma’aikatan Jihar Jigawa Kudin Hutunsu Karmar Yadda Gwamnatin Tayi Musu Alkairi.

Kudin Hutu Dai Wani Kudi Ne, Wanda Gwamnati Take Biyan Ma’aikata Fiye Da Rabin Albashinsu Kyauta A Duk Shekara.

Ma’aikata A Jihar Jigawa, Sun Nuna Farin Cikisu Da Jin Dadinsu Gamai, Da Yadda Gwamnatin Jihar Jigawa Take Biyansu Dukkanin Hakinsu Batare Da Bata Lokaciba.

Gwamna Badaru, Dama Shine Ya yi wa Ma’ikata Alkwarin Zai Dawo musu Da Kudin Hutu Idan Suka Ba shi Kuri’arsu A Lokacin Zaben 2015, Bayan Da Gwamnatin Da ta Shude Ta Soke Biyan Kudin Hutu A Jigawa.

You may also like