Ma’aikatan Jinya Sun Bawa Gwamnati Wa’adi Na Fara Yajin Aiki A yayin da ake kokarin kawo karshen yajin aikin Likitoci, Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikatan Jinya na asibitocin tarayya sun ba Gwamantin tarayya wa’adi zuwa ranar 20 ga wannan watan kan ta biya masu hakkokinsu ko kuma su shiga yajin aiki.

A cikin sanarwar da Gamayyar Kungiyoyin suka fitar sun nuna cewa gwamnati ta ki cika masu alkawari na biyansu alawus alawus dinsu da kuma yin karin girma ga membobin su da suka cancanta.

You may also like