
Asalin hoton, ZIYA PAVAL/INSTAGRAM
Wannan ce haihuwar ƴan daudun ta farko
Wasu ma’aurata ƴan daudu da ke a jihar Kerala ta kudancin Indiya, waɗanda hotunansu suka yaɗu a duniya, sun samu haihuwa, suna cike da tsantsar murna.
Ziya Paval, ta ce abokin zaman ta Zahad ya haihu ne a ranar Laraba.
Ms Paval ta bayyana labarin ne a shafinta na Instagram, inda ta wallafa hoton abin da aka haifa kusan wata guda da ya wuce.
Sun ce wanda ya haihun da kuma abin da aka haifa suna cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai ba su bayyana jinsin abin da aka samu ba.
Ms Paval da Mr Zahad waɗanda ke amfani da suna ɗaya, sun ce dama babban burinsu shi ne su samu haihuwa.
An tabbatar da cewa ba kasafai irin haka ke faruwa ba, saboda a cewar su “a iya saninmu, ba mu taɓa jin waɗanda suka ce sun haihu da kansu ba a cikin ƴan daudu na ƙasar Indiya.”
Mutanen biyu sun yanke shawarar haihuwa ne shekara ɗaya da rabi da ta gabata, a lokacin da suke kan turbar sauya jinsinsu.
A lokacin da suka wallafa hoton abin da aka haifa, sun yi godiya ga waɗanda suka taya su da addu’o’i, da kuma waɗanda suka tallafa masu.
Mutane na ci gaba da aikewa da saƙwannin taya murna ga mutanen tun bayan samun labarin ƙaruwar da aka samu.
Wanda ya haihun, Mr Zahad, wanda akanta ne, ya ce ya shirya komawa aiki bayan yin jego na wata biyu, yayin da Ms Paval za ta ci gaba da kula da abin da aka haifa.
Asalin hoton, ZIYA PAVAL / INSTAGRAM
Ana ta aika musu da sakon taya murna a shafukansu na intanet
Ziya Paval, mai shekara 21, wanda namiji ne a haihuwa amma yanzu yake daukar kansa a matsayin mace yana tare ne da Zahad, mai shekara 23, wadda ita kuma mace ce amma kuma yanzu take daukar kanta a matsayin namiji, suna rayuwa ne ta kamar saurayi da budurwa ko ma’aurata.
Sanya hotonsu da juna biyu a shafukan sada zumunta da muhawara, ya dauki hankali, inda ake ta yada shi tare da aika musu sakonnin fatan alheri.
An yi kiyasin cewa akwai ‘yan daudu maza da mata kusan miliyan biyu a Indiya, ko da yake masu rajin kare hakkinsu na ganin yawan ya fi haka.
A shekara ta 2014, Kotun Kolin kasar ta zartar da hukuncin cewa ‘yan daudu suna da dama da ‘yanci kamar kowa a kasar.
To amma duk da haka har yanzu suna fama da wariya da nuna tsangwama da shan wahala wajen samun damar yin karatu da kuma kula da lafiya.
A lokacin da Paval da Zahad suka hadu da juna shekara uku da ta wuce, dukkaninsu sun rabu da iyaye da danginsu saboda wannan dabi’a da suka dauka ta zama ‘yan daudu.
”Iyayena Musulmi ne masu bin addini sau da kafa, wanda hakan ya sa ba sa taba bari na na koyi rawa,” in ji Ms Paval, dan daudun ya ce, ”har aske min gashi suke yi don wai kada na yi kama da mace ina rawa.”
Dan daudun da ke zaman tamatar (Ms Paval) ya ce, ya bar gidansu domin ya je ya halarci wata gasa ta matasa kuma tun daga wannan lokacin bai koma gida ba.
Ya ce ya koyi rawa ne a wata cibiya ta ‘yan daudu, inda ya kware sosai har ma a yanzu yana koya wa wasu dalibai a lardin Kozhikode.
Ita kuwa ta-mijin wato Zahad, wadda ita ce ‘yar daudun da ke daukar kanta a matsayin namiji, iyayenta Kiristoci ne a garin Thiruvananthapuram, yanzu tana aiki ne a wani babban kanti.
Zahad da a yanzu ke zaman namiji a hukumance, ta bar gidan iyayenta ne bayan da ta fito fili ta gaya musu cewa ita fa yanzu ta zama ‘yar daudu.
To amma bayan da ta samu ciki, sai iyayen suka sasanta da ita ta koma suka karbe su, ita da ta-mijin a matsayin kamar ma’aurata, har ma suke ba su duk kulawa da taimakon da suke bukata.
Da farko mahaifiyar Zahad ta ba su shawarar kada su bayyana wa duniya cewa sun samu juna biyun, amma daga baya, bayan da ‘yar daudun ta amince a bayyana sai suka sanya hotuna da labarin nasu a shafinsu na Instagram.
Shi dai dan daudun (Ms Paval) da ke zaman tamatar, har yanzu ba a ji daga iyayensa ba.
Asalin hoton, ZIYA PAVAL/INSTAGRAM
Ta-miji (a hagu) da kuma dan daudun (a dama)
Shekara daya da rabi da ta gabata ne abokanan zaman suka yanke shawarar cewa ya kamata su haihu, bayan da suka riga suka fara sauyin jinsinsu, kamar yadda Ms Paval (dan daudu) ta gaya wa BBC.
A lokacin ba a kai ga cire mahaifar ‘yar daudu, Zahad ba, saboda haka ne suka dakatar da aikin sauya sinadarin kwayoyin jikinsu na namiji da kuma mace a bisa shawarar likitocinsu.
Likitocin nasu ba su da damar yin magana da manema labari, saboda haka BBC ba ta ji daga garesu ba.
‘’Da zarar sun samu haihuwar za su iya komawa kan shirin sauya sinadarin kwayoyin jikin nasu, ‘’ in ji Dr Mahesh DM, wani kwararren likita a birnin Bangalore, wanda ya yi wa irin wadannan mutane wato ‘yan daudu aiki sau da dama.
Bayan sun haihu, ma’auratan sun ce za su yi kokarin samun wani aikin da za su iya kula da kansu yadda ya kamata.
A don haka ne ‘yar daudu Paval ta ce dole ne ta kara yawan daliban da take koya wa rawa.
Ma’auratan sun ce al’ummarsu ta ‘yan daudu na maraba tare da taya musu murna.
Sai dai sun ce, “duk da haka akwai wadanda a cikin al’ummar ta ‘yan daudu da ma wadanda ba ‘yan daudu ba da suke ganin bai kamata a ce ‘yan daudu na da jariri ba,” in ji Paval.
“To amma mu ba wani abu ba ne a wurinmu.” A cewar, ‘yar daudun.