Ma’aurata Sun Kashe Kansu a Ebonyi


Ma:auratan ‘yan Asalin Garin Mgbaleze Isu, dake Karamar Hukumar Onitcha Dake jihar ebonyi sun kashe kansu bayan da’ yar takaddama ta shiga tsakanin su.

Mijin mai shekaru 36 wato Mr Chijioke Ani ya rataye kansa ne bayan yayiwa matar tasa mai shekaru 27 dukan tsiya a gonar su dake garin na Mgbelezen wanda hakan yai sanadiyyar mutuwar matar,  inda shima yaga ba amfanin rayuwa a tare dashi,  Hakan ne yasa ya rataye kansa.

Al’umar garin sun nemi ma’auran ne amma basu gansu ba har tsawon kwana daya,  inda suka yanke shawarar zuwa nemansu.

Ansamu gawarwakin ma’auratan a gonar su,  matar na kwance cikin jini shikuma mijin a rataye akan bishiya.

You may also like