Mabiya Addinin Kirista Sun Yi Bikin Kirsimeti Tare Da Gudanar Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya
Bikin na Kirsimeti ana gudanarwa ne a kowace ranar ishirin da biyar ga watan Disamban kowace shekara don tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.

Madam Afiniki Barem Bako dake bikin na Kirsimeti tace bayan tayi sujjada zata ziyarci ‘yan’uwa don basu kyaututtuka da kuma fadakar da mata muhimmancin karbar katin zabe,

Shi ma Mr Emini Blessing ya ce sun gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a kasa.

A hudubar da ya gudanar a Majami’ar Cibiyar Tauhidi ta ECWA wato ECWA Seminary Church Jos, Pastor Yakubu Yusuf Jakheng ya ce akwai begen samun canji mai inganci a Najeriya da Duniya baki daya.

A halin da ake ciki dai, mabiyan na Almasihu na ci gaba da bukukuwa wanda a yau Litinin za a ci gaba da ziyarar bada kyaututtuka wa ‘yan’uwa da abokan arziki, da ake kira Boxing Day.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like