Mabiya Darikar Shia Sun Yi Mauludin Annabi Isa a Yola


 

Mabiya darikar Shi’a sun gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haifuwar Annabi Isa Almasihu (AS) a Yola.
A rahotan mauludin da jaridar Leadership ta wallafa, Babban malami mai jawabi a taron, Muhammad Tukur Abdulhamid ya bayyana cewa da ace Musulmi da Kirista, kowa zai yi riko da karantarwar da ke cikin littafin da aka aiko masu, toh da ba za a samu sabani a tsakanin bangarorin biyu ba. Ya ce matsalolin da ake samu ana samun su ne sakamakon kauce wa karantarwar Manzannin biyu.
Shugaban kungiyar kiristoci ta jahar (CAN) Fasto Sunday Festus wanda shi ma ya halarci bikin ya bayyana cewa taron yana da muhimmanci don haka bai kamata a shirya sau daya a shekara ba, ya ce sau uku ya kamata a shirya a shekara.
Haka shima Malam Bappari Umar Kem, wakilin Kungiyar Jama’atul Nasril Islam ya yaba da shirya taron, ya ce duba da halin da kasar ke ciki, taron ya zo a lokacin da ya dace.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like