Mace ta zama shugabar dalibai a jami’ar Sokoto


Zan yi iyakar kokarina don ganin na sauke nauyin dalibai da ke kaina, duk kuwa da cewa mutane da dama na ganin kamar ba zan iya ba. Sai dai akwai kalubale kuma na shirya wa hakan. Amina Yahaya

A karon farko a tarihin jam’iar Usman Danfodio da ke Sokoto a Arewacin Najeriya, mace ta zama shugabar dalibai.

Jami’ar Usman Dandofio na daya daga cikin manyan jami’o’in kasar, kuma Sokoto ya kasance gari ne da al’ummarsa suke adawa da bai wa mata damar samun irin wadannan mukamai.

Amina Yahaya ta samu damar zama shugabar daliban ne saboda tsige shugaban daliban jami’ar da aka yi.

 

Wannan lamari dai ba kasafai yake faruwa ba musamman a jami’o’in Arewacin Najeriya.

A iya cewa ma wannan ne karo na biyu da hakan ta kasance a yankin, tun bayan da fitacciyar ‘yar siyasar nan Naja’atu Bala Muhammad ta ja ragamar shugabancin kungiyar dalibai ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sama da shekaru talatin da su ka gabata.

You may also like