
Asalin hoton, OTHER
Real Madrid na ci gaba da samun kwarin gwiwa cewa za ta kasa Liverpool, wurin takarar sayen dan wasan gaban Ingila da ke wasa a Borussia Dortmund, Jude Bellingham.
Matashin mai shekaru 19 ne a fuskar sanannar jaridar Marca ta Sfaniya, wadda ita ce ta ruwaito labarin.
Har wayau a Sfaniya din, Barcelona ta ce Frankie de Jong na daga cikin yan wasanta hudu da ba za ta sayar ba a watan da ake ciki, kamar yadda jaridar Mirror ta ambato shugaban kungiyar Joan Laporta na fada.
Can kuwa a Ingila jaridar Mail, ta ce Manchester United ta fara tattaunawa kan damar sayen mai tsaron bayan Monaco Axel Disasi wanda dan Faransa ne.
Ajax ta shirya saka fam miliyan 40 don sayen dan wasan gaban Ghana Mohammed Kudus, in ji jaridar Star.
Hakama Sky Germany, ta ruwaito cewa Manchester United ta nuna sha’awar sayen dan wasan gaban Eintracht Frankfurt da Faransa Randol Kolo Mauni.
Sai kuma Southampton mai son sayen mai tsaron bayan Everton Michael Keane, da kuma dan wasan gaban Dinamo Zagreb Mislav Orsic. (Athletic/Fabrizio Romano).
Shi kuwa dan wasan gaban Shakhtar Donetsk Mykhaylo Mudryk, ya fada wa kungiyar tasa cewa yana son ya koma Arsenal a watan Janairun da ake ciki.(90min).
Sai kuma Juventus da Borussia Dortmund da ke sa ido kan dan wasan tsakiyar Aston Villa Tim Iroegbunam, da yanzu haka ke zaman aro a Queens Park Rangers, kamar yadda jaridar Teamtalk ta ruwaito.