Mafi Yawan Kudaden Da Najeriya Take Samu Daga Neja Delta ne – Osinbajo Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa mafi yawan kudaden da gwamnatin tarayya ke samu duk suna fitowa ne daga yankin Neja Delta ta hanyar cinikin danyen mai da ake hakowa a yankin.
Ya ce sakamakon ayyukan ta’addanci na tsagerun Neja Delta wadanda ke fasa bututun mai ya janyo yawan man da ake hakowa ya ragu matuka ta yadda kudaden da ake samu ta wannan bangare ya ragu da kusan kashi 60 cikin 100.

You may also like