Mafi Yawancin Likitocin Da Sukayi Karatu A Waje Basu Da kwarewar Aiki – Ministan Lafiya


Gwamnatin tarayya ta nuna rashin Jin dadi kan sakamakon wani jarrabawa da ya tabbatar da cewa mafi yawan Likitocin da suka yi karatu a wasu jami’o’i na kasashen waje ba su da cikakken kwarewa.

Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya ce daga cikin likitoci 686 da suka zana jarrabawar wadda jami’ar Ilori ta shirya kan tantance kwarewa, likitoci 243 ne kacal suka iya cin jarrabawar. Ministan ya ja hankalin iyaye kan su rika tantance irin makarantun da za su rika kai yaransu a kasashen waje.

You may also like