Wani magidanci dan shekaru 36 mai suna Sakiru Bello ya shiga hannun’ yan sanda a sakamakon zargin da ake masa na kashe matarsa.
Sai dai Sakiru ya musanta wannan batu inda ya ce shi dai gunduwa gunduwa ya yi kawai da gawar ta bayan ta mutu.
A fadar sa “na kira ta ne a ranar 13 ga watan Fabrilu domin mu je unguwa, da mu ke kan hanya ne mai mashin ya kade mu, ta buge kanta a kasa”
Ya ce da haka ta faru ne suka koma gida, inda ta fara korafin ciwon kai, kuma bai kai ta asibiti ba saboda ba shi da kudi. Daga bisani ta mutu, a fadarsa.
Sakiru ya ci gaba da cewa daga nan ne ya rasa yadda zai yi saboda ya san dangin matar za su ce shi ne ya kashe ta. A don haka ne ya samu adda ya yayyanka gawar ta ta, ya kulle a leda, sannan ya je wani kango ya binne su daban daban.
Sai dai iyayen matar mai suna Sherifat Bello sam ba su gamsu da wannan labari ba.
Baban ta wanda shi ya kai kara wajen ‘yan sandan jahar Lagos ya ce, sai da suka yi ta neman Sakiru bayan sun nemi ‘yar sa sun rasa, amma ya yi ta musu wasa da hankali. Ya bukaci ‘yan sandan da su yi kyakkyawan binciken al’amarin.
Haka ma yayar matar ta shaidawa ‘yan sanda cewa marigayiyar kanwarta ita ke komai a gidan mijin nata wanda ya kasa katabus duk da ta saya masa mashin din kabu kabu, daga baya kuma mota bus domin ya samu abun yi.
Ta kara da cewa an raba su ne kimanin shekara daya da ta wuce bayan da kanwar ta to koka cewa mijin na yinkurin kashe ta ya yi tsafin kudi.