Magoya Bayan APC Sun Yi Tattaki Zuwa Ofishin INEC A Kano
Magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki a Kano, sun yi tattaki zuwa ofishin hukumar zabe ta INEC, don nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon zaben gwamna.

A farkon makon nan hukumar ta INEC ta ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris a Najeriya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, yayin tattakin, an ga magoya bayan dan takarar APC, Nasiru Gawuna dauke da kwalaye da aka yi rubutu iri-iri suna waka suna dosar ofishin na INEC.

“Zaben jihar Kano bai kammalu ba,” wani daga cikin masu tattakin ya ce a wani hoton bidiyo da gidan Rediyon Freedom ta watsa kai-tsaye a shafinsa na Facebook.

Hukumar INEC ta ce Abba na NNPP ya samu kuri’a 1,019, 602 yayin da Gawuna ya samu 890,705.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like