Magoya Bayan Boko Haram Na Matuƙar Raguwa – Buhari


Shugaba Muhammad Buhari ya tabbatar da cewa a duk rana magoya bayan kungiyar Boko Haram na matukar raguwa musamman yadda rundunar soja ke ci gaba da fatattakar sauran mayakan da suka makale a dajin Sambisa.

Buhari ya ce ” babu yadda za ka cusa mugun ra’ayi ga yara ‘yan shekara 14 ta yadda za su rika kai harin kunar bakin wake ga jama’a sannan ka ci gaba da kiran sunan Allah saboda dayan biyu ne; ko dai baka san abin da kake fadi ba ko kuma baka yi imani da kalmomin da kake furtawa ba”

You may also like