Wasu daga cikin magoya bayan shugaban kasa Muhammad Buhari, sun bayyana shi a matsayin “Jagora da muka yarda da shi.”
A wani taron gangami da suka gudanar a gaban ginin ofishin jakadancin Najeriya dake birnin London, yan Najeriya mazauna Birtaniya sun ce Buhari yana sake dora kasarnan akan tafarkin cigaba.
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels, Stephen Kifordu shugaban kungiyar ya ce babu wani kyakkyawan sauyi da ya wuce Buhari da Osinbajo a shekarar 2019.
Kifordu ya ce yanzu masu zuba jari suna sha’awar Najeriya, saboda yakin da Buhari yake da cin hanci da rashawa.
“Muna da shugaban kasa a Najeriya da mutane za su kalla su yarda da shi cewa idan na zuba jari a Najeriya, ba za a sace mun jarina ba,” ya ce.
Ya kara da cewa shugaban ya samu nasarar shawo kan matsalar tsaro da kuma ta tsagerun yankin Niger Delta.