Magoya bayan tsohon Shugaban PDP na kasa kuma tsohon Gwamnan Borno, Modu Sheriff a jihar Edo sun canja sheka zuwa jam’iyyar APC.
Da yake bayyana dalilinsu na canja shekar, Tsohon dan takarar kujerar Gwamnan na PDP a jihar, Matthew Iduoriyekenmwen ya ce a halin yanzu PDP ta koma jam’iyyar ‘yan danniya.