Ƴaƴan jam’iyar PDP masu yawa da kuma magoya bayan jam’iyar sun sauya sheƙa ya zuwa jam’iyar APC a Agbonda dake mazabar Ajase II a ƙaramar hukumar Irepedun ta jihar Kwara.
Masu sauya sheƙar sun alaƙanta fushinsu na sauya sheƙar kan watsi da aka yi dasu da kuma rashin alƙibla a tsohuwar jam’iyarsu.
Sakataren jam’iyar APC reshen jihar,Olabode Adekanye wanda ya karɓi masu sauya sheƙar a madadin jam’iyarsa lokacin shirin tallafawa mutane da ya shiryawa mutanen mazaɓar Ajase II.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka rabawa mutanen da suka amfana da shirin sun haɗa da keken ɗinki da kuma injin markaɗe.
Adekanye ya ce sauya shekar tsofaffin ƴaƴan jam’iyar ta PDP a yankin wata manuniya ce dake nuni da cewa gwamnatin jihar da jam’iyar APC ke jagoranta tana biya masu zaɓe bukatunsu.