Magoya Bayan Sanata Kwankwaso Sun Yi Taron Cikarsa Shekaru 60


 

Yanzu haka magoya bayan Tsohon Gwamnan Kano, kuma Sanata a yanzu, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso mai wakiltar Mazabar Kano ta tsakiya, kuma jagoran kwankwasiyya na kasa sun gabatar da makon Kwankwasiyya don tunawa da cikarsa shekaru 60 a duniya, wanda suka gabatar a makon da ya gabata.

Shi dai wannan mako, wanda aka fara tun ranar Alhamis har zuwa daren Lahadi, ya fara ne da taron mawallafan Kwankwasiyya, gabatar da jawabai da littafi, wanda ya kunshi ayyukan Kwankwaso sama da Dubu 6, wanda aka rubuta a shekara 4 kachal na hawansa na 2, wanda Hajiya Binta Rabiu Sifikin ta rubuta. Sai kuma jawabai daga daukacin tsofaffin Kwamishinoninsa da ’yan Majalisa da ke tare da shi a yanzu, da sauran dinbin magoya bayansa.

Haka kuma an gabatar da addu’o’i da taron manema labarai da kuma hirarraki a kafafen yada labarai akan dalilinsu na kasancewa da Sanata Kwankwaso, da kuma wannan mako da suka shirya a daidai wannan lokaci.

A jawabinsa ga manema labarai a ofishinsa da ke Kano, daya daga cikin dattawa a tafiyar siyasar Kwankwasiyya, Arch. Aminu Dabo ya bayyana dalilansu na tafiya da Sanata Kwankwaso. Ya ce, tafiyar tsohuwa ce, domin tun Tsohon Gwamnan yana makaranta ya fara rike mukamai, haka kuma ya zo ya yi Shugaban Majalisar tarayya a zamanin da ya ci zabe a Jam’iyar DPN zamanin IBB.

Baya ga wannan, haka a 2003 da Sanatan ya fadi a zabe, “duk mun taru muna ta tunanin zuwa kotu don nuna rashin yarda, sai Kwankwaso ya ce mu bar wa Allah, bayan haka kuma ya ce mu je mu taya Shekarau murnar cin zabe. Mu dai abin ya ba mu mamaki, amma sai muka koyi yadda da kaddara daga Allah. Amma da muka ci zabe a 2011 a karo na biyu, Tsohon Gwamna Shekarau sai ya kasa hakuri, sai da ya kai kara har kotun karshe. To wannan abin la’akari ne daga rayuwar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Shi kuwa Sakataran kungiyar Kwankwasiyya, Kwamared Baba Abubakar Umar, Tsohon Shugaban Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu, ya bayyana cewa sun hakura da komai sun bi tafiyar Kwankwaso saboda kishinsa ga mutanen Kano na tallafa wa ’ya’yan talakawa da ilimi kyauta da kuma kayatar da Kano ta kowacce fuska.

Su kuwa ’yan Majalisu Hon. Zubairu Mamuda Yarima Madobi, da Hon. Ali Isyaku Danja masu ci a yanzu da suka halarci taron sun bayyana cewa abin kunya ne a yi dokar goge sunan Kwankwasiyya a Kano. Suka ce su 26 cikin ’yan Majalisa 40 na Majalisar Dokokin jihar, duk suna nan aka yi wadannan ayyuka na Kwankwasiyya a Kano, sannan a ce wai an yi doka na cire Kwankwasiyya, to su dai suna nan tare da Sanata ba gudu ba ja da baya.

Shugabanni da dama ne suka yi jawabai na dalilan wannan rana, wadanda suka hada da Tsohon Sakataren gwamnati Jihar Kano, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, Dakta Dan Gwani, Tsohon Kwamishinan Ruwa, Hon. Alhaji Yusif Danbatta, Hon. Abba K. Yusif. Haka kuma akwai jagororin matasa, kamar su Muzambilu Lulu Gwale, Hajiya Shema’u, Alhaji Gamboliya da dai sauran magoya baya na Kwankwaso, wadanda kuma duk suka jaddada mubaya’arsu ga Kwankwasiyya.

You may also like