Magoya Bayan Shekarau Sunyiwa Hukumar EFCC Ƙawanya Yau A Jihar Kano


Dandazon Magoya Bayan Tsohon Gwamnan Kano kenan yayin da Suke Rakiya ga Tsohon Gwamnan Kano Dr. Mal. Ibrahim Shekarau tare da Allah Wadai da Gayyatar da Hukumar tayi Masa yau, a Birnin Kano.

Bisa zargin An Raba kudin zabe 2015 An Bashi naira Milyan Ashirin da biyar (25 Millions’) Zargin da Tsohon Gwamnan yasha yakaryatashi tin abaya.

Wanda hakan yasa Al’umma da dama Suke Ganin Hakan kamar Wata bita da kullane akewa Tsohon Gwamnan Saboda yana Sukar Gwamnatin Buhari.

Ganin yadda Tsohon Gwamnan yai Shekara Takwas yana Gwamnan Kano ba’a taba kamashi dalaifin Sataba Sai yanzu da ake Ganin Zaben 2019 yatawo kuma Shekarau din yana Cikin Masu Takara A PDP Shima.

‘Yan adawadai na Zargin EFCC da yaki da ‘yan PDP Ganin yadda ba’a kama Magoya Bayan APC Sai na PDP kamar yadda Wata Majiya ta Shedawa Zinariya.

You may also like