Magu Bazai Sauka Ba Har Zuwa Ƙarshen Wa’adin Mulkin BuhariMataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a jiya Talata ya shaida cewa Gwamnatin Buhari za ta cigaba da aiki tare da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC na rikon kwarya har zuwa karshen wa’adin Gwamnatinsu. Tunda Majalisar Dattawa ta ki yarda ta tantance shi. 

Osinbajo ya kara da cewa ya yi na’am da kalaman babban lauyan nan wato Femi Falana bisa cewa da ya yi cewa koda majalisa ba ta tantance Magu ba to kundin tsarin Mulkib Nijeriya ya baiwa Shugaban kasa ikon cigaba da aiki tare da Magu.

You may also like