Magu, ministoci huɗu na cikin tawagar Buhari zuwa ƙasar Habasha


Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a ranar Juma’a zai bar gida Najeriya zuwa ƙasar Habasha domin halartar babban taron shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU.

Femi Adesina mai magana da yawun shugaban kasar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta lissafa ministoci huɗu Geoffrey Onyeama na harkokin waje, Abubakar Malami ministan shari’a, Abdulrahman Dambazau ministan harkokin cikin gida, da kuma Hadi Sirika ministan harkokin sufurin jiragen sama cikin ƴan tawagar shugaban ƙasar da za su halarci taron.

Sauran su ne Babagana Monguno, mai bada shawara kan harkokin tsaro da kuma Ibrahim Magu mai riƙon muƙamin shugaban hukumar EFCC.

Ana san ran shugaban kasa Muhammad Buhari zai gabatar da maƙala a taron kan yaƙi da cin hanci da rashawa a nahiyar Afirka.

You may also like