
Asalin hoton, Getty Images
Mahaifin Ansu Fati, Bori Fati ya ce baya jin dadin yadda Barcelona ke ajiye yaron yana dumama benci.
Ya ce zai so yaron mai shekara 20 ya koma wata kungiyar da taka leda, amma a zabinsa gwara ya zauna a Camp Nou, wadda ya fara tun yana karami.
”Ina jin haushin rashin saka shi a wasa yadda ya kamata, sai dai ya buga minti daya ko biyu ko uku, hakan yana bakanta min rai,” in ji Bori kamar yadda ya sanar da wani gidan rediyo a Sifaniya.
”Ni ba zan ce sai a saka shi a wasa ba ko ta halin kaka, saboda dukkan ‘yan wasan Barca da ke ci mata kwallaye suna da kayu, kuma suna gabansa, amma ina magana ne kan Ansu Fati,” kamar yadda ya sanar da Cadena Cope.
”Muna magana ne kan dan kwallon tawagar Sifaniya mai saka riga mai lamba 10 a Barcelona, yaron da ya fara kungiyar daga La Masia.”
Ansu Fati ya fara yi wa Barcelona tamaula a 2019 yana da shekara 16 da haihuwa a lokacin, wanda ya nuna kansa a fannin tamaula.
To sai dai dan wasan ya ji rauni a gwiwar kafarsa a 2020, hakan ya sa ya yi jinya mai tsawo da yawa.
A shekarar 2021 ya karbi riga mai lamba 10 da Messi ya ajiye, wanda ya koma Paris St Germain da taka leda.