
Asalin hoton, JUDE BELLINGHAM
Mahaifin ɗan wasan tsakiyar Ingila da ke buga wa Borussia Dortmund na son Jude Bellingham ya tafi Liverpool, duk da yake Real Madrid da Man City ma suna neman ɗaukar matashin mai shekara 19.
Ɗan wasan gaban Fotugal mai shekara 23, Joao Felix – da Manchester United ke nema – ya samu ‘yancin barin Atletico Madrid a Janairun nan.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Amurka Sporting Kansas City ta yi ƙoƙarin ɗaukar Cristiano Ronaldo kafin ɗan ƙwallon mai shekara 37 ya shiga kulob ɗin Al Nassr na ƙasar Saudiyya.
Newcastle sun yi “wani gwaggwaɓan tayi” ga ɗan wasan bayan Real Madrid Ferland Mendy, mai shekara 27.
Chelsea na ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan bayan Faransa, Benoit Badiashile, sai dai kocin Monaco Philippe Clement ya yi gargaɗin cewa ba ita kaɗai ce ke son sayen ɗan wasan mai shekara 21 ba.
Mykhailo Mudryk ya ce manajan Arsenal Mikel Arteta “babban koci ne”, inda ita ma Chelsea ta bi sahun Gunners ɗin a rige-rigen sayo ɗan wasan gefen na Shakhtar Donetsk mai shekara 21.
Tottenham Hotspur ta “hau matakin farko” a ƙoƙarin sake cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Ingila da ke buga wa Sporting Lisbon Marcus Edwards, mai shekara 24.
Haka kuma Tottenham ɗin na gab da kammala wani kwanturagin fam miliyan 35 don ɗaukar ɗan wasan bayan Sporting Lisbon Pedro Porro, mai shekara 23.
Leeds United ta kusa cimma yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan baya mai shekara 24, Maximilian Wober, daga Red Bull Salzburg.
Ɗan wasan gaban Borussia Monchengladbach mutumin ƙasar Faransa Marcus Thuram, mai shekara 25, zai gwammaci zuwa Manchester United a kan Newcastle ko Aston Villa, waɗanda su ma ke son sayen sa.
Los Angeles FC ya sha gaban ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Firimiya Lig inda ya ɗauki ɗan wasan gaban Croatia, Stipe Biuk, mai shekara 20.
Juventus na sha’awar sayen ɗan wasan tsakiyar Everton mai shekara 29, daga ƙasar Mali Abdoulaye Doucoure.