Libiya: Karbe iko da cibiyoyin fidda mai


Sojojin da ke biyayya ga Janar din na Libiya wati Khalifa Haftar sun bayyana cewar sun karbe iko da tashoshin jiragen ruwa da ake fidda danyen mai a kasar.

016524874_30300

Masu aiko da rahotanni suka ce an tafaka kazamin fada kafin kaiwa ga karbe iko da tashoshin kamar yadda bangaren Janar Haftar din ya tabbatar, lamarin da ya sanya manzo musamman na MDD da a kasar Martin Kobler nuna damuwarsa game da wannan rikici. Wannan dai ba karamin koma baya baya ne ga gwamnatin kasar da ke Tripoli, wadda ke samun goyon bayan kasashen duniya duba da cewar babbar hanyar samun kudin shigarta ya koma ga hannun wanda ke adawa da ita.

You may also like