Mahara Sun Kashe Mutane 20 a Kaduna


Wasu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kai wani mummunan hari a kauyen Godogodo da ke karamar hukumar Jama’a a jihar Kaduna inda suka kashe akalla mutane 20 tare da kona gidaje masu yawa.
Da yake tabbatar da al’amarin Gwamnan jihar, Malam Nasir El Rufa’i ya bayyana harin a matsayin na rashin tausayi inda ya roki al’ummar yankin kan su kwantar da hankularsu kasancewa gwamnati za ta yi amfani da ikonta wajen zakulo wadanda suka aikata laifin.

You may also like