Mahara Sun Kashe Yan Sanda Hudu A NumanRahotanni daga Numan jahar Adamawa na cewar wasu mahara sun kashe jami’an yan sanda guda huda a shekaran jiya da dare, rundunar yan sandan jahar Adamawa ta tabbatarda aukuwar wannan lamari. 

Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN ya ruwaito maimagana da yawun rundunar Usman Abubakar yana cewar, jami’an yan sandan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke bakin aiki, kuma kawo yanzu ba’a gano maharan ba. 

Sai dai Jama’a suna hasashen cewar maharan Fulani ne wadanda suka nemi kutsawa garin domin daukar Fansar rayukan mata da yaran su da aka kashe a satin da ta gabata. 

A cewar Usman, haryanzu suna cigaba da bincike don gano masu hanu cikin wannan aika aika. 

Ga kadan daga cikin abunda yake cewa “Bama aiki da hasashen Jama’a, ina kira ga gidajen yada labaru da su gujewa masu yada jita jitar da zai kawo barkewar tashin tashina a garin na Numan” 

In bamu manta ba a satin da ta gabata ne aka samu asarar rayuka sama da Hamsin na Fulani wadanda akasarinsu Mata da Kananan yara ne a garin na Numan, wanda ake zargin  Kabilar Bachama da aikata wannan aika aika.

You may also like