Tawagar kungiyar maharba da ‘yan banga a jihar Adamawa sun yi nasarar kashe dakarun kungiyar Boko Haram bakwai da kuma kame guda a karamar hukumar Madagali, a wata arangama da suka cikin makon nan.
Rahotannin da suke fitowa daga yankin sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun kaddamar da hare-haren ne ranar asabar da ta gabata cikin dare, inda su ka kone gidaje da sassare musu amfanin gona da barnata kayan dubban naira.
Kamar yadda wata majiya ta shaidawa wakilinmu, maharani suna tsaka da cin karensu babu babbaka ne, labari ya isa ga Maharban da su ke garin Makwan wanda ke kusa da garin Gulak inda su ka same ‘yan bindigar cikin gaggawa.
Wani da abun ya faru a kan idonsa, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce an fara musayar wuta tsakanin bangarorin biyu ne da misalin 12 na dare, inda maharban su ka yiwa ‘yan bindigar biji-biji, wasunsu kuma su ka gudu da munanan raunuka.
Ya ci gaba da cewa a yayin fafatawar ne aka kashe ‘ya’yan kungiyar Boko Haram bakwai da kame wani guda, sauran kuma suka tsere cikin daji da raunuka a jikinsu.
“Maharban sun dauki kusan awa uku su na bata-kashi tsakaninsu da ‘yan bindigar, har su ka kai ga kashe bakwai da kame wani guda, saura kuma su ka gudu daji.” In ji majiyar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin daya daga cikin kwamandojin kungiyar maharban Bukar Jimeta, ya ce mutanensu sunyi nasarar kashe ‘yan bindigar Boko Haram, to sai dai baiyi wani karin bayani ba.
Da aka tuntube jami’in hulda da jama’a na runduna 28 ta sojojin Nijeriya da ke Mubi, ya ce bashi da wani masaniyar labari makamancin haka, ya ce zai tuntuba bayan ya binciki batun.