
Asalin hoton, EPA
Malawi da Madagascar da Mozambique na ci gaba da farfaɗowa daga cikin wata mahaukaciyar guguwa da ta afka musu.
Sama da mutum 400 ne suka mutu da kuma ɗaiɗaita dubbai.
Guguwar ta kasance ɗaya cikin mafiya daɗewa da aka taɓa samu a yankin ko ma duniya baki ɗaya.
Kudancin Afirka ya sha faɗa wa cikin bala’o’in guguwa da ke zuwa daga tekun Indiya amma ita wannan ta sha bamban da irin waɗanda aka saba gani saboda dalilai da dama.
Tsawon wane lokaci guguwar ta shafe tana ɓarna?
Hukumar kula da yanayi ta Faransa ce dai ta sanar da batun guguwar. An sanya mata suna Freddy a ranar 4 ga watan Febrairu da kuma ta kawo karshe a ranar 14 ga watan Maris.
Guguwar ta kasance mai karfin gaske da ta kai ga ayyana ta a matsayin barazana kuma ta shafe akalla kwanaki 36.
Sai dai, sai mun samu tabbaci daga Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya kafin mu iya cewa ko ita ce mafi daɗewa da aka taɓa samu.
Wani abu dangane da guguwar shi ne irin nisan tafiya da ta ke yi.
Ta fara afkawa ne a yankin gabar tekun Australiya, inda ta tsallaka zuwa Kudancin tekun Indiya daga gabas zuwa yamma, ɗaya daga cikin guguwa huɗu da suka yi irin haka a tarihi.
Ya ya karfinta yake?
Hanyar da ake gane karfin guguwa shi ne irin iskar da ta zo da ita.
Iskar da mahaukaciyar guguwa ta Freddy ta zo da shi tana tafiya a kilomita 260 a cikin sa’a ɗaya.
Wani abin takaici shi ne ta fi nausawa a kan ruwa.
Guguwar ta kafa tarihin zamantowa mai karfin gaske a yankin, inda ta wuce tarihin da wata guguwa mai suna Fantala ta yi a 2016.
Wannan kuma shi ne karo na farko a yankin da guguwar ta afku har sau huɗu.
Mamakon ruwan sama da ake samu a wasu yankuna ya kuma janyo zaɓtarewar gine-gine marasa galihu.
Guguwar ta yi ɓarna mai yawa da ba a taɓa ganin irinsa ba a tsawon lokaci.
Mene ne bambancin guguwa da kuma iska?
Guguwa a tekun Indiya na da karfi fiye da iskar ruwa.
Mahaukaciyar guguwar ta fara afkawa Mozambique ne a matsayin ƴar karama.
Sai dai ta kara karfi lokacin da ta sake dawowa ƙasar, sannan lokacin da ta kai Malawi, karfinta ya wuce kima – duk da cewa wurin ne ta fi yin ɓarna.
Me guguwar za ta yi gaba?
A halin yanzu, guguwar ta yi ɓarna mai girman gaske, tana kuma ci gaba da janyo mamakon ruwan sama a faɗin Mozambique da Malawi, abu kuma da zai ƙara munana batun ambaliya.
Shin sauyin yanayi ne ya haddasa afkuwar mahaukaciyar guguwar?
Wannan tambaya ce mai wuyar amsawa saboda ba a saba ganin irin guguwar ba.
Mun ga irin wannan guguwar a baya lokacin guguwar La Nina a tekun Indiya.
Hukumar kula da yanayi ta ayyana kawo karshen guguwar ta La Nina a-jere, wadda ta faro a watan Satumban 2020.
A ɓangaren sauyin yanayi, batu ne da aka sani cewa iska mai ɗumi ai rike ruwa mai yawa, don haka yawan ruwan sama da ake samu, za a iya cewa ya ƙaru ne saboda sauyin yanayi.
Ruwa mai ɗumi a cikin teku na da karfin gaske, inda yake bin iska don ƙara karfi domin janyo ƙarin ruwan sama.