Wani mai babur dauke da man fetur ya yi sanadiyar konewar wasu mutane tara a yankin Dakatsalle dake karamar hukumar Bebeji a jihar Kano. Inda mutane shida suka kone kurmus, yayin da ragowar guda ukun suke cikin halin rai-kwakwai-mutu’kwakwai a asibiti.
Lamarin wanda ya auku da ranar yau, mai babur din wanda yake dauke da jarkokin man fetur guda biyu, ya bugi wata mota ce a yayin da direbanta ke daukar fasinja a bakin hanya.
Shi dai mai babur din ya yi kokarin kaucewa wata mota ne da ta so ta buge shi, wanda a dalilin haka jarkokin da suke dauke da fetir din suka fashe a kusa da wani mai shayi har ta kai ga fetir din ya kama da wuta, ita ma motar ta kama da wuta dauke da fasinjojin dake cikinta.