Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta – INEC ta ayyana Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe.
Da yake sanar da sakamakon zaben a Damaturu babban birnin jihar, babban jami’in da ke kula da zaben, Farfesa Umaru Pate ya ce Mai Mala Buni ya lashe zaben da kuri’u 317,113 a yayin da Sheriff Abdullahi na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 104,259.